Yawancin mutane sun yarda da cewa ba
dabara bace mutum ya zabi budurwa ranar
Sallah, saboda a ranar ne kowa da kowa ya
kure a dakarsa wajen cin ado babu yadda za
ai ka gane wacce take da kyau da tsafta idan
ba da Sallah bane!Ni kuwa sai nawa ra’ayin yasha ban-ban!
A tawa fahimtar ranar Sallah shine ranar
da ya kamata mutum ya zabi abokiyar
zama!
Dalili na akan hakan kuwa shine ranar
Sallah itace ranar da kowa ya kure
hikimarsa wajen ganin ya fita fes-fes, yana
walkiya da kyalkyali da sheki, hakan ya
nuna kenan ita wacce ka zaba din wannan
shine irin kyawunta na asali wanda Allah
ya halicce ta dashi, ba wanda zaman
Nijeriya ya mayar da ita ba.
Saboda haka ashe kenan indai zaka sama
mata abubuwan yin kwalliyar to haka zata
zamo kullum kamar tauraruwar daren
goma sha hudu.
0 Comments:
Post a Comment