Showing posts with label Bayani game da watan Ramadan. Show all posts
Showing posts with label Bayani game da watan Ramadan. Show all posts

MUHIMMANCIN TASHI SAHUR

Muhimmancin sahur









Assalamualaikum waraha matullah sanun mu da sake Saduwa a cikin wan nan sabon shirin nine naku labakar S koko kamar kullum




TAMBAYA

Menene muhimmancin sahur saboda musan ma anarsa dai sauransu abinda ya dace mu sani game da sahur




AMSA 

Shi sahur abune mai matuƙar muhimmanci yanada kyau ace muna yinsa 




Manzon Allah S A W yace muyi sahur domin a cikin sa akwai wata albarka mai Yawa san nan wan nan sahur ɗin shine zai ban hanta Musulmi da Christian domin suma suna yin Naso azumin




Da ahlulkitab duk sunayin nasu Azumin shine Manzon Allah yake ban hanta azumin mu da nasu yace yin sahur shine ban banci ɗin dan haka mu kula ƴan uwa


Wani kuma yana so ya tashi amma idan baya iyawa saboda idan yaci abinci da yawa cikin sa ya ɓaci ya rinƙa damun sa da yawan kashi da dai sauransu kaga irin wannan duk bai dace ba  shiyasa baya ci.



To ƴan uwa shi addinin mu da kuke gani  wayeyyen addini ne baya takurawa kowa balle ya cutar da mutun amma idan ka fahimce shi

 


Baya taƙurawa mutun ga abinda bazai iya ko kuma idan yayi zai cutar dashi amma dai zakaga akwai hadisin Manzon Allah S A W da yake  cewa Ni'imar sahur alamar tanbayane Mafi Alkairin sahur shine da bino 


Ma'ana ana nunama sahur ba wai katashi ka cika ciki bane ka kwanta A zaka iya cin ko dan dabino ne ko kuma ruwa dan dai katashi ka albarkaci wan nan Lokacin saboda Manzon Allah S A W yana cewa masu yin sahur Allah da mala'ikunsa suna musu addu'a


To kaga kawai ka tashi wan nan lokacin kullum koda loma ɗayane kayi ka sha ruwa ko da bino dai ko ɗan ruwane ka kurɓa ko shayi kawai dai ka tabbatar kasamu abinda kasa abaki a wan nan lokacin da biyar sahur kaga zaka shiga cikin wa ƴanda Mala'iku suke yiwa addu'a



San nan kuma Allah yana maka addu'a a wan lokacin na sahur san nan kuma abu na gaba zaka irin cewa lokacin da ake yin sahur lokacin ne da Allahu subhanahu wata'ala ya ke sauko wa sama ta ɗaya tun daga sama ta bakwai ya dawo ta ɗaya yana cewa nayi ina mai neman tuna in gafar tanada ina mai neman wani abu in bashi ma ana lokaci ne mai Albarka



Dan haka tashi acikin sa yanada amfani matuƙar amfani san nan addu'a tana kar ɓuwa sosai insha Allahu


Insha Allahu anan zan tsaya sai mun haɗu ana gaba dan ha ku kasan ce da wan nan shafin mai suna www.labakar.com.ng




 



Share:

Amfanin tashi da wuri

 

FALALAR SAHUR

Assalamualaikum waraha matullah ƴan uwa barkan mu da War haka sannun mu da sake Saduwa daku adai dai wan Nan sabon labarin nine naku labakar S koko kamar kullum

Na kawo muku wata dabara ku ince wata hanya mafi sauƙi wacca wlh ya kamata ace 
Tunda kunga wan nan watan azumi ne na alkairi tunda Allah ya ɗan temake mu muna ɗan samun kuɗaɗe haka 

Ɗan uwa da fatan zaka tsaya ka saurari abinda zan faɗa da yawa wasu daga cikin mu suna saurin tashi muyi sahur wasu kuma zakaga suna ci da yawa wai dan kada suji yunwa 

Wani kuma zakaga sam baya tashi yayi wan Nan sahur ɗin kawai misalin sha biyu na dare zai ɗan ci abinci sa kuma shikenan bazai sake tashi ba sai da asuba idan kace meyasa yake haka zaice sahur ai sun barwa yara da mata to kunga wan nan sam bai dace ba 

To abunda nakeso kugane ƴan uwa shi sahur bawai maganar jarumta bace ko wai rashin jarumta maga nace tabin sunnar Manzon Allah S A W sahur abune mai matuƙar muhimmanci a musulunci 

A hadisin anas bin Malik radiyallahu anhu Manzon Allah S A W yana cewa (tasaharuf)
Fa'inna sahur Barka) ma'ana kuyi sahur saboda Akwai albarka a cikin sa ma ana manzon Allah yana cewa acikin sahur akwai albarkatu masu yawa Allah yasa mu gane


Share:

LADAR CIYARWA A WATAN RAMADAN

 



Assalamualaikum waraha matullahi Ta'ala wabara katuhu barkan mu da Saduwa A dai dai wan Nan lokacin sunana labakar S koko tare daku a wan nan lokacin


ABUNDA YA  KAMATA MUYI A WATAN RAMADAN


Ɗan uwa kama kanka nasiha kawa  Kanka wa.azi kuma muyi wa kan mu faɗa 

Ɗaya daga cikin abunda ya kamata kowa ya maida hankali shine ciyarwa kunga dai irin yanayin da wan nan azumi ya kewayo muna


Matsa nan cin yanayi na tsadar abinci Annabi S A W yace duk wanda yayi tanadin abincin bude baki wa wanda yayi azumi to Allah zai bashi lada kwatan kwacin ladar da aka bawa wanda yayi bude bakin 


Annabi yace kuma bawai za a cira bane cikin ladar shi wanda yayi wan nan azumi Bane misali ace nayi azumi kai kuma sai ka tana Dar minda abinda nayi bude baki to kwatan kwacin ladar da zan samu to kaima kwatan kwacin ladar da Allah zai baka kenan


Wa ƴanda zuciyar su bata mutu ba duk rana suna tashi da azumi kusan azumin mutun ɗari a duk rana ƴan uwa muyi ƙoƙari Mu samu wan nan damar saboda kai Kanada hali wani kuma bayada Allah ka hore muna 


Saboda wani ladar da zaka samu idan ka ciyar dashi to wata ƙila kai bazaka samu irin wan nan ladar a azumi kaba saboda yafika kiyaye ƙa idodin azumi ƴan uwa kada mu bari zuciya ta rin jaye mu mu zama ma rowata Allah ya kiyaye


Wan nan shawara ce ƴan uwa muyi ƙoƙari Musa mu ladar wan nan azumin domin ita dukiya idan baka kasheba To baza kaje da ita lahira ba koka kasheta ko karka kasheta

 

To akwai wanda yanada abinda zai iya sa adafa abincin da mutun Hamsin zasuci a duk rana har ramadan ya fita to meye abun burge wa wlh akwai wa ƴanda suke fama da kansu balle iya lansu amma mu muna nan muci abinci kala kaza kala kala dai 


Ma ƙwaftan ka suna fama da yunwa tala kawa suna fama da kansu a gari yanzu misali kaje inda ake raba abinci kaga yanda ake layi wani magidan cine amma dashi ne ake wan nan layin saboda yana cikin halin ta lauci da yunwa 


Kuma idan ka duba kunune ake raba wa wani wan nan kunun da zai karɓa shine zai yi shan ruwa dashi kuma ya aje har zuwa asuba san nan yayi sahuru dashi ya ɗauki azumi 


Meyasa bazaka cire kuɗiba ka cire ka bàsu suje su siya su dafa suci da suda iyalan su

Kasamu lada kuma dukiyar ka ta ƙara ci gaba


Allah yasa mu gane Allah yasa muyi ƙarshe mai kyau Allah kasa mu cika da imani ameen ya Allah



Share:

LADAR DA AKE SAMU A WAN NAN WATAN

 

FALALAR WATAN RAMADAN

 



Assalamualaikum ƴan uwa barkan mu da Saduwa A dai dai wan nan lokacin sunana

Abubakar s koko insha Allahu yau zamuyi


Baya nine akan Falalar azumi insha Allahu




Abuhuraira radiya lahu.anhu yace idan Azumin watan Ramadan ya shigoa ciki Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agaresa yakan zo wurin Sahabbai yace Ramadan yazo muku wan nan watan mai Albarka 




Yace Allah ya wajabta muku yin azumi a cikin wannan watan acikin sa ake bude Ƙofofin aljannah Kuma acikin sa ake bude Ƙofofin Sammai kuma acikin sa ake kulle Ƙofofin wuta san nan acikin sa ake ɗaure Sheɗanu 




Bayan haka saiya cigaba dayi musu Bayani Yace acikin sa akwai dare da yafi dare guda Dubu yace duk wanda aka haramta masa Alkairinda ke cikin wan nan wata to lallai Kam Yayi hasara an haramta ta masa alkairi 




Dukkan wanda aka haramta masa alkairin Watan Ramadana Annabi yace yayi hasara 


In kana neman abon tausayi kasa mesa to to Annabi yace Ka gama samun abun tausayi mu kiyaye dukkan mutumen da aka haram ta masa Alkairinda watan Ramadan to shi kam yashiga uku 




Dan haka waji bine muyi tsayuwar daka mu 


Tabbatar acikin wan Nan watan mu nemi alkairai wa ƴanda suke masu yawan gaske




Banda wan Nan nadaga cikin watan falalar watan Ramadan da muci riba mai girma


Mu ya wai ta ayyukan alkairi musamman wajen tsalkake zuciya ƙololuwa daga ciki


Shine a wan nan watan ake ƴan ta mutane 


Daga wuta zuwa aljannah




A dukkan wuni akwai jama.a da ALLAH yake tara sunayen su ayi list anata rubata Wa Yanzun haka insha Allahu anakai list Ɗin farko anata confirm sa sunan wane da Wane Allah yasa muna daga cikin wa ƴanda za a ƴantar Ameen ya Allah







Share:

TSARA BAR AZUMI

 

Jama'a Assalamualaikum waraha matullahi Ta'ala wabara katuhu jama'a barkan mu da Shan ruwa sunana labakar S koko saƙo zuwa ga members na wan nan shafin mai albarka


Ƴan uwa ɗan uwa ƴar uwa a dai dai wan Nan Lokacin me Kuke yine nasan bazai wuce wasu daga cikin mu sunci abinci wasu na chatting wasu game shin ko kunsan cewa yau ɗaya ga wan nan watan 

Na Ramadan to wanna kalan shiri kuka ɗaukar masa nasan zakuce babu wani shiri bayan yin niyar azumi talatin idan Allah ya yarda to kusani cewa Ramadan ba iya azumi kawai bane shikenan Ramadan watane da yake buƙatar yawan ibada da kuma yawan karatun Alqur'ani ka mata yayi ƴar uwa ɗan uwa ace kunyi ƙoƙari kun sauke Alqur'ani a cikin wan nan watan saboda hadisin Manzon Allah S A W da yazo yana cewa azumi da kuma Alqur'ani zasu ceci masu yinsa a ranar gobe ƙiyama

Azumi zai ce ya Allah nasashi jin yunwa na sashi jin ƙishirwa na hanashi cin abinda yake so arayuwa ya Allah ka bani dama na cece sa shi kuma Alqur'ani zai ce na hanashi barci kaga duk abukai ne kaga ko ya kamata ace kayi ƙoƙari kayi shi a watan Ramadan nasan wasu zasuce ta yaya zasu karan ce Alqur'ani a cikin wata ɗaya saboda izifi sittin ne kusan shafi ɗari shida da huɗu eh zakaga abun yayi yawa ga aiyuka ka kasuwa ɗan uwa zaka iya idan ka tsara shi yanda yadace saboda a wuni Kanada sallah biyar na farillah to a duk sallah ɗaya kasamu ka karanta shafi huɗu acikin Alqur'ani in ka haɗa shafi huɗu so biyar zai baka shafi ashirin in ka haɗa shafi ashirin sau talatin zai baka shafi ɗari Shida kenan kaga izifi sittin kenan ka kammala Alqur'ani kaga shafi huɗu ne kawai ya rage


Share:
Powered by Blogger.

Search This Blog

Blog Archive