Aslm barkan ku da War haka sunana labakar s ga labaran mu na safe
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce ya kamata gwamnatocin arewacin Najeriya su fito da dokoki dangane da yadda ya kamata malamai na Musulunci da na Kiristanci yin wa'azi.
"Ni da ma ra'ayina tuntuni shi ne mu da muke wa'azi ya kamata a tantance mu shin mai wa'azi ya cancanta kuma yana da ilmi."
Sheikh Daurawa ya kara da cewa "rashin tantance masu wa'azi ne ya sa ake samun rigingimun da ake ciki yanzu haka, inda za ka samu malami ya shiga gidan rediyo ya bude baki yana ta fadin abin da ya zo bakinsa.
Duk malamin da zai yi wa'azi da zage-zage to ba wa'azi yake ba ya zama dan tasha."
Ya kamata idan akwai tsari to su kansu kafafen yada labarai za su bi wajen tantance wane malami kafin ma su nemi ya yi wa'azi."
0 Comments:
Post a Comment