Showing posts with label Tarihi. Show all posts
Showing posts with label Tarihi. Show all posts

HALAYEN MAZA







*cikakken namiji shine wanda zai zama tamkar suturarki duk wanda zai kare ki daga tsiraicin, hakika a dalilin namiji da ya San hakkin ki kuma yake da zuciyar kawo miki dauki mai tausayi da rikon amana shine ya kamata ya zama uban a wajen ya'yanki.*

mafi yawan jama'a suna cewa ba a gane halin mutum sai an zauna da shi ko
kuma kaji mata suna cewa maza batukwane.

wasu matan da zarar sun kalli tsarin namiji kuma suka fahimci yana da abin
hannu shi kenan su a ganin su sun samu masoyi, basu damu da tantance halaye da dabi'u wadanda Zaki mika amanar rayuwar ki ba.

yar'uwa me yasa ba Zaki binciki hakikanin waye kike tare da shi ba.

☛ *yar'uwa ki auna ki gane cewa ya dace dake?*

*me yasa soyayya zata rudeki ta Hana ki ganin gaskiya ko kuma sauraronta ?*

*shin kin gamsu lallai wannan saurayin ya dace dake ?*

*wadannen hanyoyi ya kamata ki Bi don ki tantance waye mijinki ?*

♜ *HANYOYIN DA ZAKI GANE MASOYINKI NA GASKIYA* ♜

_akwai hanyoyin da dama da Zaki iya fahimtar ko mijinki yana kaunar ki, amma Zan kawo kadan daga cikinsu._

❯ *idan namiji yana sonki to Zaki ga yana mutunta ki tare da sanin kimar ki.*

❯ *idan namiji yana sonki, to Zaki iya canza dabi'unsa daga marasa kyau zuwa masu kyau.*

❯ *idan namiji yana sonki Zaki ga yana son zama tare da ke tare da jin dadin Hira dake.*

❯ *idan namiji yana sonki zai dinga shaukin ki kuma zai dinga gudun abinda zai bata miki rai.*

❯ *namijin dake son ki koda yaushe zai dinga ganin kin dace da shi, ba zai dinga ganin yafi ki ba.*

❯ namijin idan yana sonki hakika zai kasance mai sakin suka tare da murmushi a Gare ki, zai dunga kallon fuskarki kuma ya dinga baki labari yana
nishadantar dake.

❯ _idan so ya Kai so a zuciyar namiji da kansa Zaki ji maimaita miki cewa wance ina sonki._

❯ _namiji idan yana sonki zai dinga kishinki amma kuma ba wai irin kishin da zai takuramakiba 

*

Share:
Powered by Blogger.

Search This Blog

Blog Archive