AHALIN YANXU ANA NEMAN CIYE AREWA DA YAƘI


ALLAH SARKI ANA NEMAN CINYE AREWA DA YAƘI




 DA YAƘI SAI BAMU GANEBA KOKAƊAN
ANA NEMAN CINYE AREWA DA YAKI  

wan nan zancen abin dubawa ne Daga Wani Bawan Allah ! Yana cewa ƴan arewa

Mu sani cewa abinda yake faruwa a Arewa na ta'addancin Boko Haram, Garkuwa da mutane, harin 'yan bindiga yunwa da dai sauran su duka wannan salo ne na yaki a

 zamanance, ana yakar nahiyar Arewan 
 Nigeria ne da abinda ake kira "covert and overt operations", ta yanda wadanda ake yakar ba za su ankara ita ce a yaki Arewa wajen karya mata tattalin arziki da neman

 ilmi, a ruguza mata tsarin tsaro, a kakaba mata talauci da rashin zaman lafiya, a yayata barna da kuma yawaita mutuwa cikin al'ummah, ta yadda mutane za su kasance kowa ta kansa yake. Da wan nan

Hanyar ne suke ƙoƙarin yakin musulmi da 
Kuma arewa amma sai dai bamu gabeba
Muna ta famar zagin shuwa gabanin mu 
Ta yanda wan nan bai dace ba haka ne zasu iya yin kuskure kama zasu iya zalun tar mu ƴan arewa amma addu'a itace magani. Komai 

Sannan kuma a tabbatar da cewa lalatattun mutane cikin Arewa sune za'a basu damar zama shugabanni a Gwamnati, Malaman Addini a mayar da su 'yan barandan gwamnati, masu fadin gaskiya kuma a kassara su.

A hana noma da kiwo wajen tabbatar da rashin tsaro a Arewa, a yada makamai ko ina, a kona kasuwanni lokaci zuwa lokaci, a hana karatu da wanzuwar ilimi a Arewa, a mayar da mutane 'yan gudun hijira, a mayar da matasan Arewa 'yan ta'adda, 'yan mata a dora su a hanyar lalata da karuwanci

Wannan shine abinda makiyan mu suke shiryawa a kan Arewa, gaba daya sai nahiyar Arewa ta koma nakasassa, mutanen ciki su zamanto bayi, a mulki 'yan Arewa mulkin zalunci ba tare da 'yanci ba

Ba zamu lura ba Manyan Kasuwannin jihohin Arewa suna cin wuta, ina sakamakon bincike akan tashin wutar kasuwannin Arewa ? su wa ke sa maja wuta a manyan kasuwanni ? abin nufi 

Yanzu kawai abinda yaka mata muyi shine muriƙe addu.a insha Allahu Allah zai yi muna maganin komai kuma wani abu mune muke jawo ma kan saboda yanzu acikin mutane

Zalonci yayi yawa da cin amana da cin hanci da aikata zunubai da rashin godiyar Allah

Toh a duk lokacin da mutane suka Bar Allan da ya halicce su to dole suyi ta haduwa da jara bawa kala kala

Ya Allah ka yafe muna lai fukan mu Allah ka gafarta muna Allah ka rufa muna asiri Allah ka shirye mu Allah kasa mu tsare dokokin ka Allah ka ba mu ikon kyautata iyayen mu Allah kasa muyi kyakkyawan karshe

Insha Allahu nan zan tsaya wanda yake da ƙarin bayani toh ya duba saman hotun wan nan posting zaiga wurin comment Nagode

Kada ku manta da wan nan shifin mai suna www.labakar.com.ng 

Share:

1 comment:

Powered by Blogger.

Search This Blog

Blog Archive