Muhimmancin sahur |
Assalamualaikum waraha matullah sanun mu da sake Saduwa a cikin wan nan sabon shirin nine naku labakar S koko kamar kullum
TAMBAYA
Menene muhimmancin sahur saboda musan ma anarsa dai sauransu abinda ya dace mu sani game da sahur
AMSA
Shi sahur abune mai matuƙar muhimmanci yanada kyau ace muna yinsa
Manzon Allah S A W yace muyi sahur domin a cikin sa akwai wata albarka mai Yawa san nan wan nan sahur ɗin shine zai ban hanta Musulmi da Christian domin suma suna yin Naso azumin
Da ahlulkitab duk sunayin nasu Azumin shine Manzon Allah yake ban hanta azumin mu da nasu yace yin sahur shine ban banci ɗin dan haka mu kula ƴan uwa
Wani kuma yana so ya tashi amma idan baya iyawa saboda idan yaci abinci da yawa cikin sa ya ɓaci ya rinƙa damun sa da yawan kashi da dai sauransu kaga irin wannan duk bai dace ba shiyasa baya ci.
To ƴan uwa shi addinin mu da kuke gani wayeyyen addini ne baya takurawa kowa balle ya cutar da mutun amma idan ka fahimce shi
Baya taƙurawa mutun ga abinda bazai iya ko kuma idan yayi zai cutar dashi amma dai zakaga akwai hadisin Manzon Allah S A W da yake cewa Ni'imar sahur alamar tanbayane Mafi Alkairin sahur shine da bino
Ma'ana ana nunama sahur ba wai katashi ka cika ciki bane ka kwanta A zaka iya cin ko dan dabino ne ko kuma ruwa dan dai katashi ka albarkaci wan nan Lokacin saboda Manzon Allah S A W yana cewa masu yin sahur Allah da mala'ikunsa suna musu addu'a
To kaga kawai ka tashi wan nan lokacin kullum koda loma ɗayane kayi ka sha ruwa ko da bino dai ko ɗan ruwane ka kurɓa ko shayi kawai dai ka tabbatar kasamu abinda kasa abaki a wan nan lokacin da biyar sahur kaga zaka shiga cikin wa ƴanda Mala'iku suke yiwa addu'a
San nan kuma Allah yana maka addu'a a wan lokacin na sahur san nan kuma abu na gaba zaka irin cewa lokacin da ake yin sahur lokacin ne da Allahu subhanahu wata'ala ya ke sauko wa sama ta ɗaya tun daga sama ta bakwai ya dawo ta ɗaya yana cewa nayi ina mai neman tuna in gafar tanada ina mai neman wani abu in bashi ma ana lokaci ne mai Albarka
Dan haka tashi acikin sa yanada amfani matuƙar amfani san nan addu'a tana kar ɓuwa sosai insha Allahu
Insha Allahu anan zan tsaya sai mun haɗu ana gaba dan ha ku kasan ce da wan nan shafin mai suna www.labakar.com.ng
Thanks
ReplyDelete