TSARA BAR AZUMI

 

Jama'a Assalamualaikum waraha matullahi Ta'ala wabara katuhu jama'a barkan mu da Shan ruwa sunana labakar S koko saƙo zuwa ga members na wan nan shafin mai albarka


Ƴan uwa ɗan uwa ƴar uwa a dai dai wan Nan Lokacin me Kuke yine nasan bazai wuce wasu daga cikin mu sunci abinci wasu na chatting wasu game shin ko kunsan cewa yau ɗaya ga wan nan watan 

Na Ramadan to wanna kalan shiri kuka ɗaukar masa nasan zakuce babu wani shiri bayan yin niyar azumi talatin idan Allah ya yarda to kusani cewa Ramadan ba iya azumi kawai bane shikenan Ramadan watane da yake buƙatar yawan ibada da kuma yawan karatun Alqur'ani ka mata yayi ƴar uwa ɗan uwa ace kunyi ƙoƙari kun sauke Alqur'ani a cikin wan nan watan saboda hadisin Manzon Allah S A W da yazo yana cewa azumi da kuma Alqur'ani zasu ceci masu yinsa a ranar gobe ƙiyama

Azumi zai ce ya Allah nasashi jin yunwa na sashi jin ƙishirwa na hanashi cin abinda yake so arayuwa ya Allah ka bani dama na cece sa shi kuma Alqur'ani zai ce na hanashi barci kaga duk abukai ne kaga ko ya kamata ace kayi ƙoƙari kayi shi a watan Ramadan nasan wasu zasuce ta yaya zasu karan ce Alqur'ani a cikin wata ɗaya saboda izifi sittin ne kusan shafi ɗari shida da huɗu eh zakaga abun yayi yawa ga aiyuka ka kasuwa ɗan uwa zaka iya idan ka tsara shi yanda yadace saboda a wuni Kanada sallah biyar na farillah to a duk sallah ɗaya kasamu ka karanta shafi huɗu acikin Alqur'ani in ka haɗa shafi huɗu so biyar zai baka shafi ashirin in ka haɗa shafi ashirin sau talatin zai baka shafi ɗari Shida kenan kaga izifi sittin kenan ka kammala Alqur'ani kaga shafi huɗu ne kawai ya rage


Share:

0 Comments:

Post a Comment

Powered by Blogger.

Search This Blog

Blog Archive